IQNA

Za A Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Isra'ila A Kasar Faransa

Bangaren kasa da kasa: Mabiya addinin musulunci a kasar Faransa sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da ayyukan ta'addanci da Isra'ila take aikatawa kan al'ummar Palastinu, da kuma hankoron mayar da birnin Qods mallakin yahudawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga daga shafin internet na blogdei cewa; a ranar Asabar mabiya addinin musulunci a kasar Faransa sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da ayyukan ta'addanci da Isra'ila take aikatawa kan al'ummar Palastinu, da kuma hankoron mayar da birnin Qods mallakin yahudawa. Musulmin za su gudanar da wannan zanga-zangar ne bayan da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta himmatu wajen rushe masallacin Qods da kuma gina wata babbar majami'ar yahudawa a wurin masallacin, inda za su gudanar da zanga-zanga domin nuna wa al'ummomin duniya rashin amincewarsu da ayyukan wuce gonad a iri da yahudawan sahyuniya na Isra'ila ke aikatawa kan musulmi da kuma wurare masu tsarki da ke palastinu.


397650