IQNA

Ministan Cikin Gida Na Turkiya Ya Yi Suka Kan Hana Saka Hijabi A Kasar

Bangaren kasa da kasa: Ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiya ya bayyana cewa, hana mata musulmi saka hijabin musulunci a jami'oi da sauran cibiyoyin ilimi na kasar ya sabawa hakkokin dan adam na asasi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillnacin labaran tauhid na kasar turkiya cewa; Cubukcu Nimet Ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiya ya bayyana cewa, hana mata musulmi saka hijabin musulunci a jami'oi da sauran cibiyoyin ilimi na kasar ya sabawa hakkokin dan adam na asasi. Ministan harkokin cikin gidan kasar turkiya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa tare da wasu daga cikin mahalrta taron kare hakkokin mata, wanda kwamitin kare hakkokin mata na tarayyar turai ya shirya, ya ci gaba da cewa matan kasar Turkiya na daga cikin mata da ake danne hakkokinsu, inda aka haramta musu saka hijabi a jami'oi da cibiyoyin ilimi, ya ce saboda riko da akidar musulunci da mata da yawa da suke da ita a Turkiya, hakan ya sa sun daina karatu tare da daina halartar cibiyoyi na ilimi, domin kuwa ba zasu iya cire hijabi daga kansu ba.


397701