IQNA

Ofishin Da ke Kula da Yada Al'adun Iran a ketare Ya Halarci Baje Kolin Littafai A Jami'ar Kabul

Bangaren al'adu da fasaha;ofishin da ke kula da yada al'aduin Iran A ketare ya halarci baje kolin litattafai a Jami'ar Kabul.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a Afganistan ya halarci kasuwar baje litttafai da jami'ar birnin Kabul ta shirya na tsawon mako guda kuma ta gabatar da littafai da suka shafi fannoni daban-daban na rayuwa da tarihi da akida da siyasa tare da wani bangare na hotuna da zane masu yawan gasket da yadda suke nuna dabi'a da yanayi mai kayatarwa na Iran.

398788