Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da harkokin addinin muslunci da nazari kan ilmominsa ta Metrania, za ta gudanar da wani zaman kara wa juna ilimi kan ilmomin kur'ani a birnin Strasburg na kasar Faransa a mako mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran saphirnews cewa; Cibiyar kula da harkokin addinin muslunci da nazari kan ilmominsa ta Metrania, za ta gudanar da wani zaman kara wa juna ilimi kan ilmomin kur'ani a birnin Strasburg na kasar Faransa a mako mai zuwa. Wadnda za su halarci taron za su za su yi nazari kan tafsirin kur'ani mai tsarki da kuma bincike na ilimi kan dalilan safkar ayoyi da tarihinsu, tare da warware ma'anar wasu kalmomi na lugga da ke cikin kur'ani. A bangare guda kuma za a bude wani kwarya-kwaryan aji na koyar da karatun kur'ani ga wasu da zasu halarci taron daga kasashen turai.
399384