Bangaren kasa da kasa: Al'ummar Palastinu da ma wasu daga cikin al'ummomin kasashen larabawa sun nuna rashin amincewarsu da wani taro da yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayin ke shirin gudanarwa domin nuna kyama ga addinin msulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alyaum da ake bugawa a kasar maser cewa; Al'ummar Palastinu da ma wasu daga cikin al'ummomin kasashen larabawa sun nuna rashin amincewarsu da wani taro da yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayin ke shirin gudanarwa domin nuna kyama ga addinin msulunci. Rahoton ya ci gaba da cewa wasu daga cikin 'yan majalisar yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi na daga cikin yahudawan da suka shirya gudanar da wannan zama a cikin yankunan palastinawa da Isra'ila ta mamaye domin nuna gaba da kyama ga addinin musulunci, lamarin da palastinawa da al'ummomin larabawa da na musulmi daga sassa daban-daban na duniya suka nuna rashin amincewarsu da shi.
400155