Bangaren kasa da kasa: An ware wa musulmi wata makabarta a yankin Bourg da ke kasar Faransa, daga mai kamawa za su iya fara bizne gawawwakin mutane musulmi da suka riga mu gidan gaskiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na leprogres cewa; An ware wa musulmi wata makabarta a yankin Bourg da ke kasar Faransa, daga mai kamawa za su iya fara bizne gawawwakin mutane musulmi da suka riga mu gidan gaskiya. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin wata mai kamawa za a bude makabartar, inda babban sakataren majalisar musulmin kasar Faransa Taufiq Sharki zai samu halarta, tare da malaman addinin muslunci da wakilan kungiyoyin musulmi daga sassa daban-daban na kasar Faransa gami da limaman juma'a. Mahukuntan kasar faransa ne suka bayar da wannan dama ga muslmin yankin Bourg da su bude makabarta wadda ta kebance su saboda yawan da suke da shi a yankin, wanda kuma gwamnatin Faransa ta yi la'akari ne da takurar da musulmin yankin suke ciki wajen rufe gawawwakinsu a cikin makabartu na daban.
400393