IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Mu'ujizar Ilimin Kur'ani Wajen Shiryar Da Dan Adam

Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani zaman taro a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa kan mu'ujizar ilimin da ke cikin kur'ani mai tsarki wajen shiryar da dan adam tare da dora shi kan matsayi na kamala.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran WAM cewa; An gudanar da wani zaman taro a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa kan mu'ujizar ilimin da ke cikin kur'ani mai tsarki wajen shiryar da dan adam tare da dora shi kan matsayi na kamala. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasa da kasa da ke birnin Dubai ta shirya, ya samu halartar baki daga kasashe daban-daban, daga ciki kuwa har da fitaccen malamin nan na kasar Masar Zaglul Najjar gami da wasu jami'an huldar diplomasiyya na kasashen musulmi da ke birnin Dubai, da kuma masana kan harkokin kur'ani daga kasashen musulmi. A nasa bangaren shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani da ke birnin Dubai Iman Isma'il Abdullah ya bayyana cewa; Za a ci gaba da gudanar da irin wannan taro lokaci zuwa lokaci.


400789