Banagaren manema labarai; Maraji'ai a birnin Qum sun bayyana rashin jin dadinsu matuka gaya kan yadda aka nuna hoton Imam Hasan(AS) Da Imam Huseini (AS) a cikin wata fim a Koweiti.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Kheima ta watsa rahoton cewa: wannan fim din na nuna hotunan Imam Hasan Da Huseini (AS) wani mataki ne da bai dace ba da kuma kawo cikas kan irin sakon da ake son isarwa da kuma darasin da ke tattare a cikin wannan fim din alhali kuwa da fim din ba ta kumshe da abubuwan da za su tayar da hankali da tafi samun karbuwa da wanzuwa a tsakanin musulmai da kuma ilmantarwa.
402762