Bangaren kasa da kasa: Babban masallacin birnin Tokyo fadar mulkin kasar Japan ya zama wani wurin haduwar mabiya addinai daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Dunya Bulteni na kasar Turkiya cewa; Babban masallacin birnin Tokyo fadar mulkin kasar Japan ya zama wani wurin haduwar mabiya addinai daban-daban. Wannan masallaci dai mutanen kasar Turkiya da suke zaune a kasar Japan ne suka gina wannan masallacin tun a cikin shekara ta 1935. Da dama daga cikin mutanen kasar Japan sun nuna sha'awarsu dangane da yadda aka gina masallacin, lamarin da yake jan hankalinsu zuwa masallacin domin ganin yadda musulmi suke gudanar da harkokin ibadarsu, kamar yadda suke yin tambaya kan abubuwan da suke bukatar Karin haske kansu dangane da addinin musulunci.
402635