Bangaren siyasa da zamantakewa; A kasar Zambiya ne aka gudanar da taron tunawa da ranekun shahawadar tunawa da shahadar diyar ma'aikin Allah Muhammadu dan Abdullahi (SWA) .
Cibiyar da ke kula harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoto kan gudanar da bukukuwa na juyayin shahadar Fatima (AS) kuma tun kafin fara taron an farad a sallar Magariba da Isha'I da kuma karatun kur'ani da fassara kana daga bisani mai kula da ofishin kula yada al'adun kasar Iran a Zambiya Asadi Muwahid Wanda ya yi bayani kan matsayi da daukakar Fatima Zahra (AS) a tsawon tarihi ba za a taba mantawa da rawar da ta taka ta fuskoki daban-daban da suka shafi rayuwa da addini.
403978