Bangaren kasa da kasa: Hadaddiyar kungiyar daliban jami'a na kasashen Kuwait da Birtaniya gami da Ireland sun yanke Sahawar sayen majami'ar birnin Derby na kasar Birtaniya domin mayar da ita masallaci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar Kuwait ta Alwatan cewa; Hadaddiyar kungiyar daliban jami'a na kasashen Kuwait da Birtaniya gami da Ireland sun yanke Sahawar sayen majami'ar birnin Derby na kasar Birtaniya domin mayar da ita masallaci. Hadaddiyar kungiyar dalaban jami'a na kasashen Kuwait da Birtaniya da Ireland sun sanar da hakan ne a cikin shafin internet na kungiyar ta su, inda suka bayyana cewa sun kudiri aniyar sayen wannan majami'a da ke birnin Derby domin mayar da ita masallaci, kuma suna kiran dukkanin musulumi a ko'ina suke cikin fadin duniya da su taimaka da taimakon kudade domin ganin su ma ba a bar su a baya ba wajen gudanar da wannan babban aikin lada. Bayanin ya kara da cewa yanzu haka wasu daga cikin limaman masallatai a sassa daban-daban na kasar Birtaniya sun tara wasu kudade sun mika wa wannan kungiyar domin gudanar da wannan aiki.
403318