IQNA

Al-Azhar Ta Mayar Da Martani Kan Batun jinkirta Ayyukan Haji Da Umrah

Bangaren kasa da kasa: Bangaren kula da harkokin fatawa da bincike na jami'ar Alazhar ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya yi kakkausar suka kan neman da wani malami ya yi kan a daga lokutan ayyukan haji da Umra saboda tsoron yaduwar murar aladu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwatan ta kasar saudiyya cewa; : Bangaren kula da harkokin fatawa da bincike na jami'ar Alazhar ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya yi kakkausar suka kan neman da wani malami ya yi kan a daga lokutan ayyukan haji da Umra saboda tsoron yaduwar murar aladu. Jaridar ta ci gaba da cewa malamin day a yi wannan kira shi ne babban malamin jami'atul azhar wanda kuma shi ne ke bayar da fatawa a jami'ar Sheikh Tantawi shi ne ya yi wannan kira ga sauran malaman addinin musulunci na duniya, kan su fitar da fatawa ta bai daya domin halasta jinkirta ayyukan haji da Umra saboda tsoron yaduwar murar aladu sakamakon tafiye-tafiye da 'yan kasashen waje ke yi zuwa kasashen yankin gabas ta tsakiya, amma wannan kira ya fuskanci mayar da martini daga jami'ar ta azhar da ma wasu malaman musulmi daga sassa daban-daban na duniya.

405356