Bangaren kasa da kasa: Majalisar malamai ta kasar Bahrain ta yi Allawadai da fatawar da wasu malaman wahabiyawan saudiyya suka bayar da ke kafirta tare da halasta jinin mabiya mazhabar shi'a, majalisar ta ce babu wanda hakan zai amfanar illa makiya addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Awal da ake bugawa a birnin Manama na kasar Bahrain cewa; Majalisar malamai ta kasar Bahrain ta yi Allawadai da fatawar da wasu malaman wahabiyawan saudiyya suka bayar da ke kafirta tare da halasta jinin mabiya mazhabar shi'a, majalisar ta ce babu wanda hakan zai amfanar illa makiya addinin musulunci. A cikin wani bayani da majalisar ta fitar ta bayyana cewa; fatawar da wasu malaman wahabiyawan Saudiyya suka bayar kan kafirta mabiya mazhabar shi'a tare da halasta jininsu, musamman ma limamin masallacin Makka mai alfarma Adil Kalbani, wannan yana bayyana ra'ayin wasu 'yan tsiraru ne kawai, kuma hakan ba zai yi wani tasiri wajen raba kan al'ummar musulmi da sunan mazhaba ba.
405750