Bangaren kasa da kasa: Majalisar musulmin kasashen nahiyar Asia ta yi Allawadai da duk wani aikin wuce gonad a iri da sunan addinin musulunci a zamanta da take gudanarwa a kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Today Zaman cewa; Majalisar musulmin kasashen nahiyar Asia ta yi Allawadai da duk wani aikin wuce gonad a iri da sunan addinin musulunci a zamanta da take gudanarwa a kasar Turkiya. Rahoton ya ci gaba da cewamajalisar ta bayyana hakan ne a cikin bayanin bayan taro da ta fitar a jiya, bayan kammala zamanta a birnin Istambul na kasar turkiya, inda ta bayyana cewa ayyukan wuce gona da iri da sunan addinin musulunci abu ne mai matukar muni, kuma aikata duk wani aikin wuce gonad a iri da sunan addini daidai yake da aikin ta'addanci. Daga karshe majalisar ta yi kra ga dukkanin musulmi da su yi aiki da koyarwa irin ta addininsu, wanda ya zo wa 'yan adamtaka da fiyayyen tafarki, tare da kyamatar duk wani wanda ya mayar da addinin musulunci wata hanya ta tayar da hankali.
405676