IQNA

Rasuwar Ayatollah Bahjat Ta Dauki Hankulan Kafofin Yada Labarai

Bangaren kasa da kasa: Kafofin yada labaran kasashen larabawa sun mayar da hankali kan rasuwar babban malamamin addinin musuluncin na kasar Iran Ayatollah Ozma Haj Sheikh Muhammad takiyi Bahjat, inda suka bayyana rasuwarsa da cewa wata babbar asara ce ga dukkanin mabiya mazhabar ahlul baiti AS
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; : Kafofin yada labaran kasashen larabawa sun mayar da hankali kan rasuwar babban malamamin addinin musuluncin na kasar Iran Ayatollah Ozma Haj Sheikh Muhammad takiyi Bahjat, inda suka bayyana rasuwarsa da cewa wata babbar asara ce ga dukkanin mabiya mazhabar ahlul baiti AS. Limamin masallacin Saihat a kasar Saudiyya Abdulmohsen Namir ya bayyana cewa; rasuwar Ayatollah Bahjat Babbar asara ce ga duniyar musulumi baki daya, kuma yana mika sakon ta'aziya ga duniyar musulmi dangane da wannan babban rashi da aka yi. Ya ci gaba da cewa Ayatollah Bahjat day ace daga cikin malaman musulunci da suka shahara da kyawawan dabi'u na kamala, da kuma mayar da Allah madaukakakin sarki babban buri, wanda duniya musulmi ba za ta taba mantawa da rawar day a taka ba wajen tarbiyantar da al'umma.

406967