Bangaren kasa da kasa: Babban limamin juma'a na birnin Najaful Asharaf ya bayyana cewa; duk da cewa Imam Khomeni ya kasance a lokacin da yake gudun hijira a Najaf ya shagaltu da batutuwa na siyasa da juyin juya halin musulunci, amma kuma a lokaci guda yana gudanar da harkokinsa na ilimi tare da kyautata dangantaka da dukkanin manyan mamalan addini da ke birnin Najaful Ashraf.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na alqubanci.com cewa; Babban limamin juma'a na birnin Najaful Asharaf Hojjatol Islam Sayyid Sadruddin Al-qonaci ya bayyana cewa; duk da cewa Imam Khomeni ya kasance a lokacin da yake gudun hijira a Najaf ya shagaltu da batutuwa na siyasa da juyin juya halin musulunci, amma kuma a lokaci guda yana gudanar da harkokinsa na ilimi tare da kyautata dangantaka da dukkanin manyan mamalan addini da ke birnin Najaful Ashraf. Ya ci gaba da cewa duk da irin nauyin day a rataya kan imam a wancan lokaci na jagorantar harkokin juyin juya halin muslunciamma kuma a lokaci guda yadda yake gudanar da harkokin bayar da ilimi a Najaf tamkar babu wani gagarumin aiki da ke gabansa, kuma a cikin wannan yanayin ne da taimakon Allah ya kawo karshen tsarin zalunci da danniya na sarki shah, tare da kafa gwamnatin Islama a Iran.
407065