Bangaren Internet: Shafin internet da kafar labarai ta ware wani fili na sabke kur'ani ta hanyar Internet domin hadaya ga ruhin marigayi Ayatullahi Bahajat.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: wannan shafi na Internet yana karkashin hukumar yada musulunci da ya kawo bayanin rayuwa da ayyukan da Ayatullahi Bahajat ya gudanar a lokacin day a ke raye domin ciyar da musulunci da musulmi da kuma yada ilimi .Har ila yau kuma sun ware wani fili na sabkar kur'ani da suka yi hadayar laden ksabke kur'ani ga ruhin marigayi ayatullahi Bahajat da Allah ya yi wa rasuwa a wannan mako yana mai shekaru 96 da haifuwa a wannan duniya. Kuma rashin wannan bawon Allah ya girgiza hantar al'ummomin musulmi a duniya musamman musulmin Iran .
407627