Bangaren al'ada da zamantakewa: Komitin gwamnati mai lura da sha'anin addini a kasar Azarbeijan ya amince da kuma bawa masallacin Alhayit a birnin Baku damar ci gaba da ayyukansa a hukumce.
Daga yankin aazarbeijan ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Gunduz Isma'ilUf daya daga cikin mambobin komitin gwamnati da ke lura da ayyukan addinin a wannan kasa a wata tambaya kan shin ko gyare-gyaren da aka yi a cikin dokoki da suka shafi akida da addinai da kuma yanci da takaitawa ya shafi addinin musulunci kai tsaye kuma mai zai ce a kai san ya bayyana cewa: dangane da amasallacin Alhayit dake kusa da jami'ar gwamnati a Baku babu abin day a shafe shi kuma ba shi da matsala kuma wannan masallaci bayan ya yi rajista a hukumce zai ci gaba da ayyukansa kamar yadda ya saba.
409143