Bangaren kasa da kasa: Ofishin da ke kula da tsarawa da kuma shirya kasuwar baje koli da kuma ya zabi birnin kudus a matsayin babban birnin duniyar larabawa a wannan shekara ya wallafa wani littafi mai suna alfanul Islami abrul Usur.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga jaridar Palasdinu ta Alkudus ta watsa rahoton cewa: wannan littafi Marwan Abu Khalf ne mai bincike kuma malamin jami'ar Kudus ya rubuta tare da hadin guiwar wasu yan uwansa masu bincike da nazari tare da kuma da fassara wannan littafi a cikin yaren turancin Ingilishi.Shi dai wannan littafi ya yi bayani dalla-dalla dangane da fasaha da kwarewa da musulmi suka nuna a cikin karnoni da suka gabata.
412821