IQNA

Kotun Kasar Saudiyya Ta Saki Wani Malamin Shi'a Da Aka Kama A Kasar

Bangaren kasa da kasa: Kotun shari'ar manyan laifuka ta kasar Saudiyya ta saki malamin shi'ar nan Sheikh Ali Bin Hossein da mahukuntan kasar suka bayar da umurnin kame shi, bayan kasa tabbatar da wani laifi a kansa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga tashar talabijin ta rasid cewa; Kotun shari'ar manyan laifuka ta kasar Saudiyya ta saki malamin shi'ar nan Sheikh Ali Bin Hossein da mahukuntan kasar suka bayar da umurnin kame shi, bayan kasa tabbatar da wani laifi a kansa. Tun a cikin watan da ya gabata ne mahukuntan kasar Saudiyya suka bayar da umurnin kame sheikh Ali Bin Hossain Al-imar daya daga cikin malaman mabiya mazhabar shi'a na kasar Saudiyya, bisa zarginsa da tara taimako domin gina wuraren tarukan addini na mabiya mazhabar shi'a da kuma masallatai a yankin Al-ihsa. Jmai'an tsaron kasar saudiyya bisa umurnin mahukuntan kasar sun jima suna daukar matakan takura mabiya mazhabar shi'a da ke kasar, wadanda kuma su ne marassa rinjaye, tare da hana su gudanar da harkokin addini daidai da koyarwar mazhabrsu.

412767