Bangaren rahoto: Za a gudanar da tarukan tunawa da cika shekaru ashirin da rasuwar Imam Khomeini a garuruwan daban-daban na kasar hadaddiyar daular larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen hadaddiyar daukar larabawa ya habarta cewa; Za a gudanar da tarukan tunawa da cika shekaru ashirin da rasuwar Imam Khomeini a garuruwan daban-daban na kasar hadaddiyar daular larabawa. Bayanin ya ci gaba da cewa gungun Iraniyawa mazauna kasar hadaddiyar daular larabawa da ma wasu daga cikin mutanen kasar da suke goyon bayan tsarin musulunci na Iran, za su gudanar da taruka a garuruwa daban-daban da ke cikin kasar, domin tunawa da rasuwar Imam. Bayanin ya ce za a gabatar da jawabai daban-daban dangane da rayuwar Imam da kuma irin rawar da ya taka wajen fadakar da al'ummar musulmi dangane da halin da musulunci ya samu kansa a ciki.
415130