IQNA

Tsarin Banki A musulunci Zai Ci Gaba Da Mamaye Tsarin Kudi Na Duniya Har 2015

Bangaren kasa da kasa: Toni Piras masani kwararrai kan sha'anin tattalin dan kasar Britaniya ya bada labarin yadda tsarin tsarin banki na musulunci zai ci gaba da tasirin a tsarin kudi na duniya har zuwa shekara ta 2015.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna a Iran ce ta nakalto daga jaridar Katar mai suna Alraya cewa ; Toni Piras ya bayyana cewa: masu saka hannayen jari daga kasashen musulmi a shekara ta dubu biyu da goma za su shiga da kutsawa a cikin harkokin hada-hadar kudade na duniya kuma hakan zai ci gaba da wanzuwa har zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.Kuma tsarin bankoki na musulunci zai mamaye tsarin kudi na duniya yayin da hukumce-hukumce na shari'ar musulunci a wannan bangare za su ci gaba da taka rawar gani.

419498