Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani taro na kasa da kasa wanda Turkiya za ta dauki nauyin bakuncinsa dangane da yaduwar ayyuka na fasaha da fannonin ilimi a kasashen musulmi, wanda za a gudanar a birnin Istanbul.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar kula da shirya tarukan kasa da kasa da suka danganci addini a kasar turkiya cewa; Za a gudanar da wani taro na kasa da kasa wanda Turkiya za ta dauki nauyin bakuncinsa dangane da yaduwar ayyuka na fasaha da fannonin ilimi a kasashen musulmi, wanda za a gudanar a birnin Istanbul.Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da ma wasu kasashen da ban a musulmi ba, domin bayyana irin ci gaban da aka samu ta fuskacin fasaha a kasashen musulmi. Kasar turkiya dai na daya daga cikin kasashen musulmi da suke taka muhimmiyar rawa ta fuskacin yada fasahar musulunci.
421710