IQNA

Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Nuna Wariya A Otrish

Bangaren kasa da kasa:Kimanin mutane dubu biyar ne a Viyan babban birnin kasar Otrishe suka gudanar da zanga-zanga yin Allah wadai da nuna wariya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga Dunya Bulteni ta watsa rahoton cewa: a lokacin gudanar da wannan zanga-zanga da aka bawa taken Kaso na Haske inda mutane sama da dubu biyar a wannan birni suka bayyana adawarsu da duk wani lamari day a shafi nuna wariya da banbanci a tsakanin al'umma ta fuskar launin fata ko yare da harshe ko yankin da suka fito da cewa wannan wata babbar kansa ce da ke tsakanin al'umma.

422264