IQNA

An Fara Taro Kan Sulhu Da Adalci Da Tattaunawa Ta Bai Daya A Duniya A Ostriya

Bangaren kasa da kasa;an fara taro kan sulhu da adalci ta hanyar tattaunawa ta bai daya a duniya da cibiyar da ke kula da sulhu a duniyar musulmi a jiya a Ostriya.
Bayan ta nakalto daga bangaren hulda da jama'a na wannan hadin guiwar da ke kula da sulhu a duniyar musulmi ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya watsa rahoton cewa: wannan taro zai kwashe kwanaki biyu ana gudanar da shi tare da halartar masana da kwararru daga Iran da kuma sauran kasashe na duniya kamar Faransa,Otrish,Jamus,Kurwasiya da Italiya da kuma jawabai daban daban.

422416