IQNA

An Nuna Wasu Kayyakin Fasahar Musulunci A Jami'ar Birnin Madina

Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani taron nuna kayyakin fasahar musulunci da suka hada da rubutun kur'ani da kuma alluna da ke bayyana ci gaban kimiyyar musulunci a jmai'ar birnin Madina.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alnadwah ta kasar saudiyya cewa; An fara gudanar da wani taron nuna kayyakin fasahar musulunci da suka hada da rubutun kur'ani da kuma alluna da ke bayyana ci gaban kimiyyar musulunci a jmai'ar birnin Madina. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani ta sarki fahad ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan taro, inda aka fitar da wasu daga cikin muhimman kayan tarihi da ke bayyana fasahar addinin musulunci tun tsawon shekaru sama da dubu daya da suka gabata. Taron yana samun halartar masana dake gudanar da bincike kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi tarihin musulunci, daga cikin kasar da ma wajen kasar.


423509