Bangaren ilimi da fasaha: ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a Nigeria ya dauki nauyin fassara littafin Jihadun Akbar na imam Khomeini ® a cikin harshen Hausa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa ofishin da ke kula da yada al'adun iran a Nigeria musamman da ked a birnin Lagos nan bad a jimawa ba zai watsa littafin Jihadul Akbar da Imam Khomeini ® ya rubuta day a kumshi shafi saba'in da daya da aka fassara a cikin harshen Hausa,kuma za a isar da littafin ga mabukata masu alaka da addini. Har ila yau ofishi ya fassara littafin day a kumshi du'a'in Komeil a cikin harshen Yoroba inda yan kabilar Yoroba suka nuna bukatar hakan.
423496