Bangaren siyasa da zamantakewa: babban sakataren shirya tarorruka na jama'ar larabawa a kasar Labanon ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake kiran kungiyoyi a kasar ta Labanon da su hada kansu wajen tunkarar shirin Amerika da Haramtaciyar kasar Isra'ila .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce daga kasar ta Labanon ta watsa rahoton cewa; babban sakataren shirya tarorruka na jama'ar larabawa a kasar Labanon ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake kiran kungiyoyi a kasar ta Labanon da su hada kansu wajen tunkarar shirin Amerika da Haramtaciyar kasar Isra'ila .Har ila ya yi nuni da yadda rashin hadin kai a tsakaninsu zai iya kawo cikas ga manufar kasar ta Labanon da hakan zai bawa makiyi damar cimma mummunar manufarsa cikin sauki hankali kance.Amma hadin kai zai taimaka masu tunkarar makiyinsu da hana shi cimma manufarsa ta boye da ta zahiri.
424303