Bangaren al'adu da fasaha; A cikin darasin akhalak kyawan dabiu da ya ke gabatarwa, babban malamin addinin msulunci a Iran ya bayyana cewa; ya kamata al'ummar musulmi su yi amfani da watan Rajab da damar da suke da ita a cikin wannan wata mai albarka domin karfafa imaninsu da ruhinsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren kula da harkokin ilmi da al'adun musulunci da cibiyar kula da buga littafai ta Darulhadis cewa; A cikin darasin akhalak kyawan dabiu da ya ke gabatarwa, babban malamin addinin msulunci a Iran ya bayyana cewa; ya kamata al'ummar musulmi su yi amfani da watan Rajab da damar da suke da ita a cikin wannan wata mai albarka domin karfafa imaninsu da ruhinsu. Bayanin ya ci gaba da cewa watan rajab daya ne daga cikin atannin da musulunci yak e bayar da muhimmanci wajen yawaita ibadar ubangiji a cikinsu, a kan haka bai kamata musulmi su yi sake da wannan damar da Allah ya hore musu ba. Shehin malamin ya mayar da hankali ne wajen bayyana hadisai na falalar ibada a cikin wannan wata mai alfarma.
426616