IQNA

An Gudanar Kan Ayyukan Imam Musa Sadr A Kasar Labanan

Bangaren rahoto; Daya daga cikin malaman jamhuriyar musulunci ta Iran Sayyid Ja'afar Fatemi Nosh Abadi ya rubuta a cikin wata makala cewa; Imam Musa Sadr wani ramzi na yada ilimi da gwagwarmaya da 'yantar da labanan daga danniya da mamaya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Daya daga cikin malaman jamhuriyar musulunci ta Iran Sayyid Ja'afar Fatemi Nosh Abadi ya rubuta a cikin wata makala cewa; Imam Musa Sadr wani ramzi na yada ilimi da gwagwarmaya da 'yantar da labanan daga danniya da mamaya. Ya ci gaba da cewa Imam Musa Sadr ya taka gagarumar rawa da musulunci ba zai taba mantawa da ita ba, ta fuskacin yada ilimin addinin musulunci da wayar da kan musulmi. Haka nan kuma daga cikin muhimman ayyukan Imam Musa Sadr dad a tarihin duniya ba zai taba mantawa da sub a akwai batun kafa tafarkin gwagwarmaya da ya yi Labanan, wanda hakan shi ne mafarin gwagwarmayar al'ummar wannan kasa, wadda ta basu karama da martaba a idon duniya baki daya.


427418