IQNA

An Buga Tare Da Yada Littafin Irfanin Musulunci A Kasar Rasha

Bangaren al'adu da fasaha; An buga tare da yada littafin nan irfanin musulunci wanda marubucin nan Marita shugaban bangaren falsafar gabacin duniya a birnin Moscow ya rubuta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An buga tare da yada littafin nan irfanin musulunci wanda marubucin nan Marita shugaban bangaren falsafar gabacin duniya a birnin Moscow ya rubuta. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafin ya kawo muhimman batutuwa da suka shafi samuwar ubangiji da kuma tabbatar da hakan a mahanga ta addinin musulunci gami da kwararn dalilai masana falsa muslmi suka dogara a kansu. Ya kuma rubuta littafin a cikin shafuka dari biyu da saba'in. Daga cikin muhimman abubuwan da ya yi tsokaci a kansu akwai batun tabbatar da samuwar ubangiji ta hanyar tajrubar ilmi da kuma samuwa ga baki daya.

429574