Bangaren rahoto; Za a gabatar da wasu daga cikin shirye-shiryen da cibiyar kula da harkokin ilmin na'ura mai kwakwalwa ta Iran ta shirya, dangane da ulmomi da suka shafi ilmin sanin zamantakewar dan adam.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen lardin Qom ya habarta cewa; Za a gabatar da wasu daga cikin shirye-shiryen da cibiyar kula da harkokin ilmin na'ura mai kwakwalwa ta Iran ta shirya, dangane da ulmomi da suka shafi ilmin sanin zamantakewar dan adam, wanda za a gabatar a wajen taron gasar karatu da hardar kur'ani ta kasa da kasa da za a gudanar a birnin Tehran. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin na'ura mai kwakwalwa a Iran ta dauki wani salo na bayyan ailmomin addini ta na'ura mai kwakwalwa, domin yada ilimi cikin sauki ga al'ummomin muulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri za a nuna wa masu halartar taron gasar kur'ani da za a gudanar a Iran.
436120