IQNA

A Farkon Watan Sha'aban Ne Za A Wanke Dakin Allah Da Ruwan Zamzan

Bangaren kasa da kasa: A farkon watan Sha'aban ne za a wanke Dakin Allah da ruwan zamzam da kuma Khalid Alfaisal bin Abdul Aziz amirin birnin Makka zai halarta.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga majiyar labarai ta Nasij cewa; Salih bin Abdul Rahman Alhasin shugaban da ke kula da Ka'aba da Masallacin Manzon Allah (SWA) kan wannan labari ya bayyana cewa; a wannan shekara kamar yadda aka saba a kowace shekara a wani buki na musamman za a wanke Ka'aba da ruwan Zam-zam da aka hada da ruwan Gulab na musamman da ake tatsowa daga Flawa.

436552