Bangaren al'adu da fasaha; Za a gudanar da maulidin Imam Hossein AS a hubbaren Shah Abdulazim da ke garin Ray na kasar Iran, wanda zai samu halartar malamai da masu karatun wakokin yabon manzon Allah da iyalan gidansa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar yada al'adu da ilmi da ta Dar alhadis cewa; Za a gudanar da maulidin Imam Hossein AS a hubbaren Shah Abdulazim da ke garin Ray na kasar Iran, wanda zai samu halartar malamai da masu karatun wakokin yabon manzon Allah da iyalan gidansa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron dai za a gudanar da shi ne kamar yadda aka saba gudanar da tarukan addini a wannan hubbare. Daga cikin muhimman abubuwan da za a yi akwai bayanai daga malamai, sai kuma addu'oi da za a karanta da munajati.
438362