IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Sha Biyar Ga Sha'aban A Azarbaijan

Bangaren al'adu da fasaha; Za a gudanar da tarukan ranar sha biyar ga watan sha'aban a kasar Azarbaijan, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin ta kasar za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshensa na birnin Baku cewa; Za a gudanar da tarukan ranar sha biyar ga watan sha'aban a kasar Azarbaijan, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin ta kasar za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron maulidin Imam Hussain a ranar lahadi da ta gabata, inda aka gabatar da laccoci da nufin karfa musulmi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ma duk mai son jin tarihin Imam Hussain da yadda rayuwarsa ta kasance da sauran iyalan gidan manzon Allah SAW da suka rayu tare da shi a zamanin imamancinsa.

440768