Bangaren al'adu da fasaha; Addinin musulunci ya bayar da matukar muhimmanci ga harkar rubutu wajen dora al'umma kan sahihin tafarki tare da wayar da kan mutane, da kuma kyautata zamantakewar rayuwarsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na reshen lardin markazi cewa; Addinin musulunci ya bayar da matukar muhimmanci ga harkar rubutu wajen dora al'umma kan sahihin tafarki tare da wayar da kan mutane, da kuma kyautata zamantakewar rayuwarsu. An buga tare da yada hadaddun makalolin da aka rubuta kan kur'ani mai tsarki da kuma tafsirin ma'anonisa, wanda aka gabatar a kasar Labanan.
Bayanin ya ci gaba da cewa Kwamitin wanda ya hada kungiyoyi da cibiyoyin addinin musulmunci sama da 40 daga sassa daban-daban na kasashen duniya, zai yi dubi ne a zaman nasa na birnin Tripoli kan muhimman batutuwa da suke ci ma al'ummar musulmi tuwo a kwarya a cikin wannan zamani, da hakan ya hada da cin zarafin da ake yi wa musulmi da mabiya addinin musulunci a wasu kasashe na yammacin turai, tare da daukar matakan da suka dace da nufin kawo karshen hakan.444975