Bangaren al'adu da fasaha: za a gudanar da taro na wayewar Iran a cikin shekaru dubu goma a birnin Istambul.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: za a gudanar da wata kasuwar baje kolin nuna kayan tarihi da duk wani abu da ke dangantaka da waye a tsawon tarihi na al'ummar Iran a cikin shekaru dubu goma da suka gabata .Kuma wannan kasuwar baje kolin za a gudanar da ita ne a birnin istambul na kasar Turkiya inda baki na kasashen waje musamman al'ummar Turkiya da ta Iran za su halarta.
469729