Bangaren fasaha; Gwamnain Iran a bayyana cewa a shirye take ta wadata dukkanin dakunan karatun kasar Canada da littafan addinin Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafi internet na CIN cewa; Gwamnain Iran a bayyana cewa a shirye take ta wadata dukkanin dakunan karatun kasar Canada da littafan addinin Musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren kula da harkokin karatu da dakunan karatu na kasar Iran, ya sanar cewa Iran din a shirye take ta wadata dukkanin dakunan karatu na kasar Canada da kowadanne irin littafai na addinin musuluni. Bayanin ya ce wannan na daya daga cikin irin kokarin da Iran din take na wadata dakunan karatu a sassa daban-daban na duniya da littafai na addinin Musulunci. 472014