Bangaren al'adu da fasaha: Mata musulmi da ke sanya Hijabi a Yammacin Turai na fuskantar matsaloli da takurawa.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna daga kasar Turkiya bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Al'alam ta watsa rahoton cewa: Uzdamir a matsayinta na mace ta farko da ke sanye da hijabi a majalisar dokokin kungiyar tarayyar Turai ta fuskanci tsananin suka da matsaloli masu yawa kawai saboda tana sanye da hijabi na Musulunci wannan malama musulma yan kasar Turkiya ta ci gaba da cewa: daga lokacin da ta samu shiga wannan azure na majalisar dokokin tarayyar Turai ta fuskanci takurawa da kutatawa ba iyaka.
472010