IQNA

Zanga-zangar Kin Jinin HKI A Istambul

Bangaren kasa da kasa: a jiya ne masallata a masallacin Fatih a birnin Istambul suka gudanar da zanga-zangar kin jinin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma ta'addancinta na kisan gilla kan fararen hula Palasdinwa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto da kungiyar hadin kan al'umma mai zaman kanta ta watsa rahoton cewa: dariruwan fararen hula ne suka gudanar da zanga zangar kin jinin bakaken ayyukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila musamman ayyukanta na wuce gonad a iri da kuma rusa gidajen palasdinawa da ke zaune a yankin har ila yau mahalarta wannan zanga-zanga sun yi ta rera taken hadin kai a tsakanin musulmi da kuma na fallasa ta'addancin haramtacciyar kasar Isra'ila.

473303