IQNA

Taro Kan Hajji Da Sakon Farilla Ta Allah Ga Al'ummar Duniya

Bangaren tunani da ilimi: ofishin yada al'adun Iran a Indiya ne ya shiraya wannan taro kan hajji da sakon da ke cikinta.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa' Karim Najafi mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Indiya ne a wani taron manema labarai kan wannan taro kan matsayin hajji da sakon da wannan farilla ta Allah ke dauke da shi ga al'ummar duniya ya bayyana cewa: ta hanyar shirya taron kasa da kasa a kasashen Afrika ta kudu,Senegal da Indiya shi kanshi wani sako ne mai cike da muhimmanci ga al'ummar duniya musamman al'ummomin wadannan kasashe da wadanda suka halarci taro ko fahimtar abubuwa da aka tattauna a gurin taro ko hakikanin hajji.

476402