Bangaren al'adu;Mai bada fatawa a kasar Suriya a cikin wani jawabi ne day a gabatar ya bada shawarar ware wata rana da yammaci za su nemi gafarar Kudus.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga kasar Suriya ta nakalto majiyar labarai ta gwamnati Sana na cewa: Ahmad Badrul dine ta gabatar da wata shawara da a ciki yake neman kasashen yammcin turai da su ware wata rana ta neman afuwar Kudus kan yadda suka yi sanadiyar kumcin da wannan birni da masallacin kudus da al'ummar Palasdinu mazauna wannan birni.Ya kara da cewa yin haka zai zama wani hambasa da wani salo da zai zama darasi ga sauran al'ummomi a nan gaba.
479711