Bangaren nazari da tunani: malama kuma shugaban jami'ar mata a jami'ar tarbiyat Mudarris a cikin wani jawabi da ta gabatar a gaban yan jami'a iraniyawa mazauna wannan kasa ta Filipine inda ta yi bayani kan Wilaya a Musulunci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: Garawi Na'ibi malama kuma shugaban jami'a a a lokacin da ta ke bayani kan muhimmancin wilaya a tsarin addinin Musulunci ta ja hankalin yan jami'a Iraniyawa da ke zaune a wannan kasa da su bawa wannan bangare muhimmancin gaske da kuma bayyana masu irin yadda Musulunci ya bawa wannan lamari muhimmanci da kulawa ta musamman har ila yau ta yi nuni da ayoyin kur'ani da suka yi bayani ga mumunai da suka nuna biyayya ga ma'aikin Allah da kuma yadda tarihi ya tabbatar da haka da kuma ma'anar ayar da ke magana kan waliyun amr da cewa tana nufin imam Alibin Abi Taliba (AS).
479555