Bangaren siyasa da zamantakewa: Jakadan Iran a Labanon ya gana da mai fitar da fatawa a kasar ta Labanon.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna daga Labanon ya watsa rahoton cewa: Muhammad Rida Shibani a wata ganawa day a yi da Muhammad Rashid Kabani sun tattauna kan sauyi da canje-canjen siyasa da ake cikin a halin yanzu a kasar da kuma sauran lamurra da suka shafi yankin baki daya musamman lamarin Palasdinu.Jakadan jamhuriyar Musulunci a Beirut bayan wannan ganawa a wani taron manema labarai ya bayyana cewa:ta'addanci da zalunci irin na dabbancin yahudawan sahayoniya kan al'ummar Palasdinu za su yi nazarinsa da ganin irin matakan da suka dace su dauka.
480736