Bangaren rahoto; An bude wani shafin internet na mazhabar iyalan gidan manzon Allah a karon farko, wanda wasu daga cikin daliban addinin muslunci da ke birnin Isfahan na kasar Iran suka bude.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Isfahan cewa; An bude wani shafin internet na mazhabar iyalan gidan manzon Allah a karon farko, wanda wasu daga cikin daliban addinin muslunci da ke birnin Isfahan na kasar Iran suka bude. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar bude wannan shafi bat a rasa nasaba da kokarin da dalibai suke yi tare da hadin gwiwa da cibiyar yada addinin musulunci ta Iran domin kara fahimtar da al'ummomi daban-daban koyarwar iyalan gidan manzon Allah. 482003