IQNA

A Garin Kalmakhu Na kasar Suriya Ne Za A Gudanar Da Makon Al'adu Na Iran

Bangaren al'adu: za a fara gudanar da makon al'adu na Iran a garin Kalmakhu na kasar Suriya kuma za a ci gaba da gudanar da wannan mako har tsawon mako guda cir.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoto kan bukukuwan fara wannan mako na al'adun Iran a wannan gari da kuma aka samu halartar wasu wakilai da mahukumta na Iran da kuma mambobin kimitin shawara na shugaban jam'aiyar garin da kuma malumman jami'a da marubuta da mawaka da wasu yan jami'a da suka halarci gurin wannan buki.

481898