IQNA

A Gobe Ne Za A Fara Taro Na Kasa Da Kasa Kan Kudus A Koweiti

Bangaren kasa da kasa;a kasar Koweiti ne za a gudanar da taro na kasa da kasa kan Kudus.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga jaridar kasar Koweiti Alfais ta watsa rahoton cewa: a gurin wannan taro na kwanaki biyu an gayyaci malumman jami'o'I ,masana da masu bincike kan al'amuran da suka shafi Palasdinu daga kasashen daban daban na duniya domin halartar wannan taro na kasa da kasa a koweiti kan Kudus. A gurin wannan taro dai mahalarta taron za su yi bincike da gabatar da bayanai kan halin da al'umma da kuma masallacin kudus ke ciki biyo bayan takurawa da kumcin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta janyo musu da kuma nuna masu wuce gonad a iri a fili.

486602