IQNA

An Fara Taro Kan Salla Karo Na Sha Takwas A Jamkaran

Bangaren tunani da ilimi:A Masallacin Jamkaran da ke Birnin Qum aka fara taro kan salla karo na sha takwas.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ne ta watsa rahoton cewa; wannan taro an fara bude shi da fara karatun kur'ani said Abazar Wahidi makaranci na kasa da kasa kuma wanda ya zo na daya a gasar olumpik na gasar kur'ani da hadisi ta kasa da ksa da jami'ar Almustapha (SWA) al'alami ke shiryawa. A ci gaba hujatul Islam walmuslim Sa'id limamin birnin Qum ya karanto sakon jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran da wannan taro na wannan shekara an ba shi taken matasa da salla da kuma bayani kan muhimmancin gudanar da irin wannan taro kan salla da kuma matsayinta a addini da kuma yadda ke haskaka zucciyar muslmi musamman mumuni.

487833