Bangaren al'adu da fasaha: a Jamus ne aka wallafa da watsa wani littafi mai suna Iran kasar gado da ofishin yada al'adun Iran a wannan kasa ya dauki dawainiyar bugawa da watsa wannan littafi.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; a kasar Jamus ne aka wallafa da watsa wani littafi mai suna Iran kasar gado da ofishin yada al'adun Iran a wannan kasa ya dauki dawainiyar bugawa da watsa wannan littafi. Shi dai wannan littafi ya kumshi shafi dari da tisi'in da biyu da kuma da taimakon David Ishtaronakh da Ali Musawi wannan littafi aka rubuta shi inda ya yi bayani kan yankuna Iran na asali da ked a tsawon tarihi na al'adu da addini da kuma bayani kan tekun fasha da yankuna irin su shush,Isfahan,Tahtai Jamshid da manyan biranai na kasar Iran.Har ila yau wannan littafi ya kumshi hotuna dari da bakwai .
489510