Bangaren da ke kula da harkokin kur'ani: Ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a Nijeriya a lokacin ganawarsa da mukaddashin mai tsara shirye-shirye ga mata da kananan yara a gidan talbijin din NTA ya bayyana shirinsa na na shirya wani shiri na karatun kur'ani ga yara kanana.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa: Azimi Nasr Abadi mai kula da ofishin yada al'adun Iran a Nijeria a lokacin ganawarsa da Amina Muhammad Abdulrahim mukaddashin mai kula da shirye-shiryen talbijin ga yara kanana da mata a gidan talbijin din NTA ya bayyana cewa; ya bayyana shirinsa na na shirya wani shiri na karatun kur'ani ga yara kanana.
532386